2 John

1Daga dattijon zuwa ga uwar gida zababbiya da yayanta, wadanda nake kauna da gaskiya, ba ni kadai ba, amma da dukan wadanda sun san gaskiya - 2domin gaskiya da take cikinmu za ta kuma kasance tare da mu har abada. 3Alheri da jinkai da salama za su kasance tare da mu, daga Allah Uba da kuma daga Yesu Almasihu Dan Uba, a cikin gaskiya da kauna.

4Na yi murna sosai sa’anda na sami wadansu yayanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda muka karbi wannan umarni daga Uba. 5Yanzu ina rokon ki, uwar gida, ba kamar ina rubuta maki sabon umarni ba, amma wannan da muka samu tun da can, cewa mu kaunaci junanmu. 6Wannan kuma itace kauna, cewa mu yi tafiya bisa ga umarnin sa. Wannan shine umarnin, daidai kamar yadda kuka ji da fari, da cewa ku yi tafiya a cikinsa.

7Gama masu yaudara sun fito a duniya, wadanda ba su yarda cewa Yesu ya zo cikin jiki ba. Wannan ne mayaudari da kuma magabcin Almasihu. 8Ku dubi kanku, domin kada ku rasa abubuwan da mu duka muka yi aiki a kansu, amma domin ku karba dukan sakamon ku.

9Duk wanda ya ci gaba da tafiya ba cikin koyarwa Almasihu ba, ba shi da Allah. Wanda ya zauna cikin koyarwar kwa yana tare da Uban da kuma Dan. 10Duk wanda ya zo wurinku, ba tare da wannan koyarwar ba, kar ku karbe shi cikin gidanku, kada ma ku gaishe shi. 11Domin duk wanda ya gaishe shi ya yi tarayya da shi kenan cikin miyagun ayyukan sa.

12Ina da abubuwa dayawa da nake so in rubuta maki amma al’kalami tawada da takarda baza su iya daukar su duka ba. Amma duk da haka ina begen zuwa gare ki domin mu yi magana fuska da fuska, domin farin cikn mu ya zama cikakke. 13Yayan yar’uwarki zababbiya suna gaishe ki.

Copyright information for HauULB